Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tarayyar Kasashen Afirka Zata Fara Taron Kolin Kwanaki Biyu Yau Litinin - 2003-02-03


Sabuwar Tarayyar Kasashen Afirka, TKA, zata fara taron kolin kwanaki biyu yau litinin a kasar Ethiopia.

Shugabanni da wakilan kasashe fiye da 35 ake sa ran zasu tattauna rikice-rikice kamar na Ivory Coast, Burundi da Kwango-Kinshasa. Shugabannin Libya da Afirka ta Kudu da Zimbabwe da kuma Sudan suna cikin masu halartar taron.

Har ila yau, za a tattauna batun yaki a Iraqi, yayin da ake nuna damuwar irin illar da zai iya yi wajen hauhawar farashin man fetur a duniya.

haka kuma, shugabannin zasu tattauna yadda za a iya karfafa irin rawar da Kungiyar ta Tarayyar Kasashen Afirka zata taka. A shekarar da ta shige aka kafa wannan kungiya a birnin Durban, a kasar Afirka ta Kudu.

XS
SM
MD
LG