Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijeriya Da Kamaru Suna Tattaunawa A Abuja... - 2003-02-05


Nijeriya da Kamaru sun fara zagaye na biyu na tattaunawa kan batun rikicin yankin Bakassi a Abuja, babban birnin Nijeriya.

Wakilai daga kasashen biyu sun bayyana kudurinsu na samo hanyar lumana ta warware wannan rikici nan da 'yan kwanaki kadan dake tafe. Makasudin wannan tattaunawa da suka fara jiya talata, shine tsara yadda zasu shata tsawon iyakarsu a yankin.

Majalisar Dinkin Duniya, MDD, ta kafa wata hukumar hadin guiwa a bara domin warware wannan rikici na Bakassi, a bayan da Nijeriya ta ki yarda da wani hukumcin kotun Duniya wanda ya bai wa kamaru mallakin wannan yanki. Nijeriya ta ce alkalan sun nuna son kai.

An yi imanin cewa akwai man fetur da gas mai yawan gaske a yankin na Bakassi, wanda kuma yake kewaye da teku mai kifaye da dimbin yawa. Nijeriya ta ce ta damu da 'yan kasarta wadanda sune akasarin mazauna yankin na Bakassi.

Nijeriya da kamaru sun yi zagayen farko na wannan tattaunawa da MDD ta shirya cikin watan Disamba a Yaounde, babban birnin Kamaru.

XS
SM
MD
LG