Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Tawayen Liberiya Sun Doshi Babban Birnin Kasar - 2003-02-05


'Yan tawayen Liberiya sun doshi Monrovia, babban birnin kasar, a bayan da suka kwace wasu muhimman garuruwa a arewa maso yamma.

Shaidu sun ce an gwabza fada jiya talata, 'yan kilomitoci a arewa da birnin Monrovia. An ga motocin a-kori-kura suna garzayawa da sojojin gwamnati zuwa bakin daga.

A cikin 'yan kwanakin nan, 'yan tawayen kungiyar "Liberians United for Reconciliation and Development" ko L.U.R.D. a takaice, wadanda ke arewacin kasar, sun gwabza da sojojin gwamnati a garuruwan Tubmanburg da Klay. Dubban mazauna garuruwan suna gudu.

A lokacin da ake kai wannan farmaki dai, shugaba Charles Taylor ba ya kasar, yana halartar wani taron kolin kasashen Afirka a Ethiopia. Har ila yau, wannan farmaki ya zo ana shirye-shiryen zaben shugaban kasar da za a yi nan gaba a Liberiya.

Ministan tsaron Liberiya, Daniel Chea, yayi rokon da a kwantar da hankula.

A halin da ake ciki dai, 'yan tawayen sun ce a shirye suke su kwace birnin Monrovia acikin mako guda, sun kuma yi kira ga shugaba Charles Taylor da ya sauka domin kaucewa zub da jini.

Yau shekaru ke nan 'yan tawayen suna kokarin hambarar da shugaba Taylor. Sun taba kai farmaki har zuwa inda suke a yanzu dab da Monrovia a watan Mayun bara, kafin sojojin gwamnati su tura su baya.

XS
SM
MD
LG