Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bush Da Manyan Baki Sun Karrama 'Yan Sama Jannatin Columbia - 2003-02-05


Shugaba Bush ya lashi takobin cewa Amurka zata ci gaba da aikinta na binciken sararin samaniya, duk da hasarar jirgin jigila a samaniya na Columbia tare da 'yan sama jannatinsa su 7 da aka yi ranar asabar.

A wajen wani taron tunawa da karrama 'yan sama jannatin da aka yi jiya talata a Jihar Texas, Mr. bush 'yan sama jannatin su 7 sun cimma mafarkin da Bil Adama ya jima yana yi na bincike sararin samaniya.

Baki da dama tare da 'yan sama jannati sun halarci wurin wannan taron da aka yi na karrama 'yan sama jannatin Columbia a Cibiyar Binciken Sararin Samaniya ta Johnson dake Houston a Jihar Texas.

A kofar shiga cikin cibiyar kuma dubban Amurkawa sun taru domin jimami, yayin da ake watsa taron kai tsaye ta tauraron dan Adam ga 'yan sama jannati ukun dake cikin Tashar Binciken Kimiyya a can Sararin Samaniya.

A halin da ake ciki, Hukumar Binciken sararin Samaniya ta Amurka, NASA, ta ce rahotannin tsintar wasu garewanin jirgin jigilar na Columbia a Jihar California, sun nuna cewa ashe jirgin ya fara wargajewa yamma sosai da inda aka zata da fari.

XS
SM
MD
LG