Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Saddam Ya Ce Babu Ruwansa da Kungiyar al-Qa'ida - 2003-02-05


Shugaba Saddam Hussein an Iraqi ya musanta cewa akwai hulda a tsakaninsu da kungiyar 'yan ta'addar al-Qa'ida ta Osama bin Laden.

Shugaban na Iraqi ya bayyana wannan furuci a cikin wata hirar da wani dan jaridar Ingila kuma tsohon dan siyasa Tony Benn yayi da shi ma gidan telebijin na Britaniya. Shugaba Saddam ya ce ai idan har akwai wata dangantaka tsakanin Iraqi da kungiyar al-Qa'ida, to kuwa da gwamnatinsa ba zata ji kunyar bayyanawa ba.

Har ila yau, ya sake jaddada cewa Iraqi ba ta mallaki makaman kare-dangi ba, ya kuma zargi Amurka da Britaniya da laifin shirya kai farmakin soja kan Iraqi domin kawai kwadayin da suke da shi na mallakar man fetur na Gabas ta Tsakiya.

Gidan telebijin na Channel 4 na Britaniya shi ya watsa wannan hirar da Mr. Benn yayi da shugaban na Iraqi a ranar lahadin da ta shige.

XS
SM
MD
LG