Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

...Manyan Wakilan Kwamitin Sulhun MDD Kuwa Sun Ce Har Yanzu Sun Fi  Kaunar Ci Gaba Da Ayyukan Bincike, Duk Da Shaidar Da Mr. Powell Ya Gabatar - 2003-02-06


Da alamun shaidar da Mr. Powell ya bayar gaban Majalisar Dinkin Duniya, MDD, ba ta gamsar da sauran wakilan Kwamitin Sulhu ba, musamman masu kujerun dindindin. A yanzu Faransa da Rasha da kuma China kira suka yi kan a karfafa ayyukan binciken makamai a Iraqi.

Wakiliyar Muryar Amurka, Jenny Badner, ta ce wadannan kasashe uku, duka masu ikon hawa kujerar-na-ki, suna son a ci gaba da aikin binciken makamai, duk da shaidar da Mr. Powell ya ce ta nuna yadda Iraqi take yaudarar sufetocin.

Faransa, wadda ke kan gaba cikin sahun masu yin adawa da gwabza yaki da Iraqi, ta ce ba wai sam ba za a iya daukar matakan soja ba, amma kuma ministan harkokin wajenta, Dominique de Villepin, ya ce da farko, ya kamata a ninka yawan sufetocin makaman sau biyu ko sau uku, a kuma kara yawan ofisoshin bincike na yankuna a cikin Iraqi. Har ila yau ya bada shawarar da a kafa wata hukuma ta musamman wadda zata ringa sanya idanu kan wuraren da aka riga aka bincika.

ACT: DE VILLEPIN: "We must move on to a new stage and further strengthen the inspections given the choice..."

FASSARA: Tilas ne mu gusa ga sabon mataki na karfafa ayyukan binciken makamai, ganin irin zabin da muke da shi na daukar matakan soja ko kuma gudanar ad ayyukan binciken da ba su da tasiri. Tilas mu zabi hanyoyin karfafa ayyukan binciken sosai. KARSHEN FASSARA

CI GABA: Rasha da China sun bayyana yardarsu da irin wannan matakin. Ministan harkokin wajen Rasha, Igor Ivanov, ya ce kwararru na kasa da kasa ne ya kamata su nazarci shaidar da Mr. Powell ya gabatar, sannan su kuma sufetocin dake Iraqi su bincika gaskiyar lamarin. Ya ce ya kamata a bar sufetocin su ci gaba da ayyukansu.

ACT: IVANOV: "The main point is that our efforts continue to be geared to doing everything possible......"

FASSARA: babban batu dai shine ya kamata mu ci gaba da bada himma ga kokarin tabbatar da karkon ayyukan binciken makamai, ayyukan da suka nuna cewa suna da tasiri kuma suka samar da kafa ta aiwatar da kudurorin Kwamitin Sulhun MDD ba tare da nuna karfi ba. KARSHEN FASSARA

CI GABA: Daga cikin wakilai 15 na Kwamitin sulhun MDD, 'yan kalilan ne kawai suke goyon bayan matsayin Amurka a kan wannan batu. Britaniya, kasar da ita kadai ce a cikin Kwamitin take goyon bayan Amurka gadan gadan, ta ce Mr. Powell ya gabatar da shaida kwakkwara kan Iraqi. Sakataren harkokin wajen Britaniya, Jack Straw, ya ce idan har Iraqi ta ci gaba da kin hada kai da sufetocin, to tilas ne a cewarsa, Kwamitin sulhun ya aikata abinda yayi barazanar yi.

XS
SM
MD
LG