Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Mahajjata Miliyan Biyu Suke Hawar Arafat... - 2003-02-10


Musulmi miliyan biyu dake gudanar da aikin Hajjin bana zasu yi salla da addu'o'i yau litinin a Dutsen Arafat dake wajen birnin Makkatul Mukarrama, yayin da ake shirin kammala aikin Hajjin.

Annabi Muhammad (s.a.w.) yayi hudubarsa ta karshe a dutsen na Arafat, kuma an yi iamni da cewa tsayuwar da ake yi a wurin tamkar kwaikwayon ranar tashin kiyama ne, ranar da Musulmi suka yi imanin cewa halittu zasu tsaya gaban Ubangiji domin fuskantar sakamakon ayyukan da suka yi lokacin rayuwarsu a duniya.

A jiya lahadi, mahajjatan sun ziyarci dakin Qa'aba a Makka, kafin su tafi su kwana a Mina.

Aikin Hajjin na bana, yana zuwa a daidai lokacin da Amurka take ta kara girka sojoji masu dimbin yawa domin kai farmaki kan kasar Iraqi. Mahajjatan na bana suna bayyana adawarsu da yaki tare da kin jinin Amurka, abinda ya sa hukumomin Sa'udiyya suka dauki matakan tsaro sosai.

Ita ma dai Amurka ta sanya cibiyoyin tsaronta cikin zaman shirin ko ta kwana a bisa wasu rahotannin leken asirin dake cewa watakila za a kai hare-hare kan cibiyoyin Amurka a lokacin aikin Hajjin.

Nan gaba cikin makon nan za a kammala aikin Hajjin da yin bukukuwan hadayar Sallar Layya, ko eid-al-Adha, inda za a yanka dabbobi a bada sadakar naman ga talakawa a fadin duniya.

Addinin Musulunci ya bukaci Musulmi da su gudanar da aikin Hajji akalla sau daya a rayuwarsu idan har suna da koshin lafiya da kuma halin yin hakan.

XS
SM
MD
LG