Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahajjata 14 Sun Mutu Bayan Da Aka Tattake Su... - 2003-02-11


Mahajjata 14 sun mutu jiya talata a bayan da aka tattake su a waniw urin aikin ibada a wajen birnin Makka.

Wasu mutane da dama sun ji rauni a Mina, lokacin da mahajjata suke gudanar da daya daga cikin ayyuka masu muhimmanci lokacin aikin Hajji: jifar shedan.

Wannan aiki na jifar shedan ya zo a daidai lokacin da Musulmi a fadin duniya suke bukukuwan Sallar Layya, lokacin da ake yanka dabbobi ana rarraba naman ga talakawa a fadin duniya.

Shugaba Bush ya bada wata sanarwa a jiya talata inda yake fadin cewa Sallar ta zo a daidai lokacin da duniya take fuskantar kalubale da kuma dama mai muhimmanci. Ya ce Amurka zata ci gaba da yin aiki tare da Musulmi da mabiya dukkan addinai wajen tabbatar da wanzuwar zaman lafiya da 'yanci da kuma dama.

XS
SM
MD
LG