Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Zata Dauki Nauyin Ayyukan Jinkai Idan Yaki Ya Barke Da Iraqi - 2003-02-14


Amurka da Majalisar Dinkin Duniya, MDD, sun yarda cewa Amurka ce zata fara gudanar da ayyukan jinkai a kasar Iraqi idan har ita Amurka ta jagoranci farmakin soja kan Iraqi domin raba kasar da makamai.

Jakadan Amurka a MDD, John Negroponte, ya ce Amurka zata kara yawan kudin da take bayarwa domin shirye-shiryen tallafawa kasar Iraqi idan yaki ya barke.

Mukaddashin babban sakataren MDD mai kula da harkokin ayyukan jinkai, Kenso Oshima, ya ce 'yan Iraqi da yawansu zai kai miliyan 10 zasu iya bukatar agajin abinci a lokacin yaki da kuma bayan yakin.

Mr. Oshima ya jaddada cewa koda yake ana yin wannan shiri a yanzu haka, har yanzu babban sakataren majalisar, Kofi Annan, yayi imani da cewa za a iya warware wannan rikici ta ruwan sanyi.

XS
SM
MD
LG