Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Tsaron Amurka Sun Ce Zaratan Sojojin Amurka Sun Fara Aiki A Asirce A Cikin Iraqi - 2003-02-14


Jami'an tsaron Amurka sun ce wasu kananan bataliyoyin zaratan sojojin Amurka sun riga sun shiga cikin Iraqi domin share fagen gwabza yaki.

Jami'an suka ce yau fiye da wata guda ke nan zaratan sojoji suna kai da komowa a cikin Iraqi, suna tuntubar masu yin adawa da gwamnatin Saddam Hussein, cikinsu har da Kurdawa.

Jami'ai suka ce zaratan sojojin suna share hanya ta yadda sauran sojojin Amurka zasu iya kama yankuna masu yawa cikin sauri da zarar shugaba Bush ya bada umurnin gwabza yaki.

Ana sa ran cewa kwamandan sojojin Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya, Janar Tommy Franks, zai gana da shugaba Bush yau Jumma'a a fadar White House domin nazarin shirye-shiryen yaki kafin ya tafi can yankin Gulf.

XS
SM
MD
LG