Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ayyuka Sun Tsaya Cik A Birnin Washington - 2003-02-16


Wani gagarumin hadarin dake tafiya a hankali ya rufe akasarin yankunan tsakiya da gabar gabashin Amurka da dusar kankara mai yawan da ya kai sentimita 60.

Dusar kankarar ta ci gaba da zuba lahadi kama daga yankin kwazazzabin Ohio har zuwa jihohin gabas ta tsakiya, ciki har da nan birnin Washington, inda masana yanayi suka ce rabon da a ga dusar kankara mai munin wannan ya kai shekara goma.

A can kuryar arewacin Amurka, wannan hadari ya haddasa gudajin kankara da dusar kankarar da suka sa aka rufe filayen jiragen sama, aka jinkirta tafiyar jiragen kasa, yayin da hanyoyin mota suka zamo masu hatsarin gaske.

A yayin da wannan hadari ya doso nan gabashin Amurka a jiya lahadi, ayyuka sun tsaya cik a nan birnin Washington, da Philadelphia da wasu manyan birane masu yawa. Jami'ai a wannan yanki sun roki jama'a da su guji fitowa waje, su kuma kaucewa hanyoyin mota har sai zuwa tsakar rana yau litinin a lokacin da ake zaton duaar kankara zata daina zuba, ko kuma zata ragu.

XS
SM
MD
LG