Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Thabo Mbeki Yace Zai Taimakawa Iraqi Wajen Kwance Damara - 2003-02-19


Shugaba Thabo Mbeki na Afirka ta Kudu ya ce gwamnatinsa zata tura wasu masana kimiyyar nukiliya zuwa Iraqi kafin karshen wannan makon, domin su taimakawa hukumomi a birnin Bagadaza cika sharrudan MDD na kwance damarar yaki.

Shugaba Mbeki ya fadawa majalisar dokokin kasarsa a birnin Cape Town cewa masana kimiyyar zasu taimaka wa Iraqi a kowane fanni na kwance damarar yaki, domin tabbatar da cewa kasar ba ta da makaman kare-dangi.

Shugaban na Afirka ta Kudu ya bayyana adawa da duk wani yakin da Amurka zata jagoranci kaiwa kan Iraqi, amma kuma ya ce tilas ne shugaba Saddam Hussein yayi aiki da dukkan kudurorin MDD da suka nemi kasar ta lalata muggan makamanta.

A cikin shekarun 1970, hambararriyar gwamnatin turawa 'yan wariyar launin fata na Afirka ta Kudu ta fara gudanar da shirye-shiryen kera makaman nukiliya, da na guba da na yada kwayoyin cuta.

Amma kuma a shekarar 1994, shekarar da bakaken fata masu rinjaye suka amshi ragamar mulki, gwamnatin turawan ta bada sanarwar kammala lalata dukkan makaman kare danginta da ta fara tun 1989.

XS
SM
MD
LG