Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Kimanin 130 Suka Mutu Lokacin Da WAni Mutum Ya Cunna Wuta A Jirgin Karkashin Kasa - 2003-02-19


Hukumomi sun ce wutar da wani mutum ya cinna da gangan ta kashe mutane kimanin 130 dake tafiya cikin wasu jiragen karkashin kasa guda biyu a birnin Daegu a Koriya ta Kudu.

An kasa tabbatar da zahirin yawan wadanda suka mutu a saboda wasu daga cikin gawarwakin mutanen sun kone kurmus ta yadda ba za a iya gane su ba. Wasu fasinjojin su fiye da 130 sun ji rauni, ta hanyar kuna ko kuma shakar hayaki.

'Yan sanda suka ce wani mutum ne ya cinna wutar ta jiya talata ta hanyar kyasta wuta cikin kwalin madara dake cike da mai, tare da wurgawa cikin taragun jirgin. Jirgi na biyu da ya isa wannan tasha a daidai lokacin ma ya kama da wuta.

Hukumomi suna yin tambayoyi ma wani mutum mai shekaru 56 da haihuwa wanda aka sani da tabuwar hankali. Shaidu sun nuna shi ma 'yan sanda a asibiti lokacin da ya je neman maganin kunar da yayi. Suka ce sun ma yi kokarin hana shi aikata wannan mugun aiki lokacin da yake kokarin sanya wuta jikin kwalin madarar.

Bakin hayaki yayi ta fitowa na tsawon sa'o'i da dama daga ramukan shakar iska na wannan tashar karkashin kasa ta Chungang-ro dake birnin Daegu, abinda ya kawo cikas ga masu aikin ceto.

XS
SM
MD
LG