Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Ya Ce zanga-Zanga Ba Zata Hana Gwabza Yaki Da Iraqi Ba - 2003-02-19


Shugaba Bush ya ce ba zai kyale zanga-zangar da ake yi a fadin duniya ko kuma adawar wasu kawayen Amurka su hana gwabza yaki da kasar Iraqi ba.

Mr. Bush ya ce yaki dai shine zabin karshe. Ya ce ya kamata Kwamitin Sulhun MDD ya tilasta yin aiki da kudurorinsa da suka bukaci Iraqi ta lalata dukkan makamanta na kare-dangi. Fadar White House ta ce watakila a cikin makon nan zata gabatar da sabon kuduri gaban Kwamitin sulhun wanda zai nemi bada iznin yin amfani da karfin soja a kan Iraqi.

Firayim minista Tony Blair an Britaniya ya ce kiyawar da Iraqi tayi ta mutunta kudurorin kwance damara na MDD, hujja ce ta kai mata farmakin soja. Amma sauran wakilan Kwamitin Sulhun majalisar suna yin adawa da gwabza yaki.

Fadar White House ta ce akasarin kasashen Turai, im ban da Faransa da Jamus, suna goyon bayan matsayinta game da Iraqi.

Wadannan al'amura na jiya talata sun zo a daidai lokacin da Kwamitin sulhun MDD ya fara tattaunawar kwanaki biyu a game da rikicin Iraqi.

XS
SM
MD
LG