Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar Ta Kulla Yarjejeniyar Sayarwa Da Iraqi Sinadarin Hada Bam Na Nukiliya A Asirce - in ji Amurka - 2003-02-21


Jami'an Amurka da na Majalisar Dinkin Duniya, MDD, sun ce Jamhuriyar Nijar ta kulla wata yarjejeniya a asirce domin sayarwa da Iraqi sinadarin hada makamain nukiliya, kamar yadda ta yi shekaru 20 da suka shige.

A cikin wani rahoton MDD da Muryar Amurka ta samo, jami'an majalisar sun ce sau biyu Nijar tana aikewa da Iraqi wani irin sinadarin karfen Uranium mai kaifi a shekarar 1981 da 1982.

Jami'an Amurka sun shaidawa Muryar Amurka cewa a shekarar 2000, Nijar ta sanya hannu kan wata yarjejeniyar domin sayarwa da Iraqi karin ton 500 na wannan sinadarin nukiliya. Shi dai irin wannan samfurin karfen Uranium mai kaifi ana yi masa kirari da sunan "Yellowcake", kuma ana yin amfani da shine wajen hada makamin nukiliya.

Amma kuma jami'an sun bayyana cewa babu wata shaidar cewa an turawa Iraqi wannan karf3e na Uranium tun shekarar ta 2000.

A can baya Nijar ta musanta sayarwa da Iraqi wani sinadarin hada nukiliya. Har yanzu dai hukumomi a birnin Yamai ba su maida martanin wannan sabon zargi ba.

A kwanakin baya darekta-janar na Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya, Mohammed el-Baradei, ya shaidawa Kwamitin sulhun MDD cewa an ce akwai wata kasar Afirka dake taimakawa Iraqi a kokarinta na sayen karfen Uranium. Sai dai el-Baradei bai fadi sunan kasar ba.

Nijar ita ce kasa ta uku a duniya a cikin masu samar da karfen Uranium a bayan Canada da Australiya. Wani kamfanin kasar Faransa mai suna COGEMA shine ke gudanar da akasarin manyan wuraren hakar karfen na Uranium a Jamhuriyar Nijar.

XS
SM
MD
LG