Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Manyan Coci-Cocin Britaniya Sun Kalubalanci Halalcin yakar Kasar Iraqi - 2003-02-21


Shugabannin manyan coci-coci biyu na kasar Britaniya sun bayyana tababar halalcin yin yaki da kasar Iraqi.

Babban limamin cocin Ingila, watau Archbishop na Canterbury, Rowan Williams, da babban limamin cocin Roman Katolika na Ingila, watau Archbishop na Westminster, Cormac Murphy-O'Connor, duk sun yi kiran da a bai wa sufetocin makamai karin lokaci domin su gudanar da ayyukansu a Iraqi.

Manyan limaman kiristocin biyu na Ingila sun bayar da sanarwa a jiya alhamis inda suke bayyana damuwa kan irin illar da ba a sani ba yaki zai haifar a fagen siyasa da kuma tagayyarar mutane.

Sun yi kira ga dukkan bangarorin da abin ya shafa da suyi aiki ta hannun MDD, suna masu fadin cewa yin hakan zai kawar da bala'in gwabza yaki. Har ila yau sun yi kira ga Iraqi da ta hada kai sosai ta hanyar aiki da kudurorin MDD da suka bukaci da ta kwance damarar yaki.

Shi dai firayim minista Tony Blair na Iraqi yayi ta gabatar da hujjar cewa aiki ne na halal a cire shugaba Saddam Hussein daga kan karagar mulki. Firayim ministan zai gana gobe asabar a birnin Rum da Paparoma John Paul na biyu, mutumin da shi ma ya bayyana adawa da kai wa Iraqi harin soja.

XS
SM
MD
LG