Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Hafsan Mayakan Saman Pakistan Tare Da Mutane 16 Sun Mutu A Hadarin Jirgin Sama - 2003-02-21


Babban hafsan mayakan sama na kasar Pakistan, Mushaf Ali Mir, da wasu mutane 16 sun mutu a lokacin da jirgin saman da suke ciki ya fadi jiya alhamis.

Babban hafsan, tare da matarsa da wasu manyan hafsoshi bakwai tare da ma'aikata 8 na jirgin sun rasu a lokacin da jirgin sufurin nasu ya fadi a kusa da garin Kohat, mai tazarar kilomita 250 a yamma da birnin Islamabad.

Babban hafsan tare da tawagarsa suna kan hanyarsu ta zuwa duba wani sansanin mayakan sama ne dake kusa da bakin iyakar kasar da Afghanistan.

Gwamnatin pakistan ta ce ta kafa wata hukumar bincike domin gano musabbabin faduwar jirgin.

XS
SM
MD
LG