Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tuhumi Tsohon Shugaban Kasar Zambiya Da Laifin Zarmiya - 2003-02-24


Hukumomin Zambiya sun kama tsohon shugaban kasar, Frederick Chiluba, suka tuhume shi da laifin zarmiya.

An bada belin Mr. Chiluba yau litinin a Lusaka, babban birnin kasar, bayan da aka tuhume shi da aikata laifuffuka 60 na sata.

Kamawa da tsare Mr. Chiluba ya biyo bayan tambayoyin da hukumar yaki da zarmiya da cin hanci ta Zambiya tayi masa sau da dama a baya. An yi masa tambayoyi ne bisa zarge-zargen cewa a lokacin da yake kan karagar mulki daga 1991 zuwa 2002, yayi rub da ciki kan kudaden gwamnati domin amfanin kansa.

A makon da ya shige, kotun kolin Zambiya tayi watsi da rokon da Mr. Chiluba yayi mata na ta maido masa da kariyar da yake da ita ta gurfana gaban shari'a, kariyar da majalisar dokokin kasar ta dage a watan Yulin bara.

Har ila yau, gwamnatin kasar ta yanzu ta tuhumi ministocinsa da dama da laifuffuka na zarmiya, a wani bangare na yaki da zarmiya da cin hanci a kasar.

XS
SM
MD
LG