Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Saddam Hussein Ya Ce Ba Zai Taba Yin Gudun Hijira Ba - 2003-02-26


Shugaba Saddam Hussein na Iraqi ya ce ya gwammace ya mutu a kan ya bar kasarsa, ya kuma ce ba zai cinna wuta a rijiyoyin mai na Iraqi idan Amurka ta kai ma kasar hari ba.

Shugaba Saddam ya yi wannan furuci cikin wata hirar da gidan telebijin na Amurka mai suna CBS yayi da shi, wadda aka watsa bangarenta jiya talata. A yau laraba gidan telebijin din zai sanya cikakkiyar hirar.

Shugaban na Iraqi yayi watsi da ra'ayin gudun hijira domin kaucewa yaki, yana mai cewa, "zamu mutu cikin kasar nan, zamu kuma kare mutuncinmu, irin mutuncin da ake bukata, kuma a gaban jama'armu."

Har ila yau, shugaban an Iraqi ya ce kasarsa ba ta taba yin hulda da Osama bin Laden ko kuma kungiyar ta'addanci ta al-Qa'ida wadda aka dorawa alhakin hare-haren 11 ga watan satumba ba.

XS
SM
MD
LG