Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Musulmi Zasu Yi Amfani Da Man Fetur A Zaman Makami Domin Hana Yaki A Iraqi - In Ji Mahathir Mohammad - 2003-02-26


Firayim minista Mahathir Mohammed na Malaysia ya ce kasashen Musulmi sun yarda zasu nazarci yin amfani da arzikinsu na man fetur a zaman makami domin hana yin yaki a Iraqi.

Malam Mahathir ya ce wakilan Kungiyar Kasashen Musulmi ta Duniya da su gana yau laraba a birnin Kuala Lumpur sun yarda cewar watakila zasu yi amfani da man fetur a zaman makami. Amma kuma ya jaddada cewar babu wata shawarar da aka cimma.

malam mahathir yayi kashedin cewa ya kamata kasashen na Musulmi suyi hattara wajen yin amfani da man fetur a zaman makami, a saboda yin hakan zai iya haddasa sakamako mai hadarin gaske.

Kasashe masu arzikin man fetur irinsu Sa'udiyya da Kuwaiti da Iran suna cikin kasashe kimanin 50 da suka halarci wannan taron gaggawa na ba-zata da aka kira a bayan da aka kammala taron kolin kasashen 'yan babu-ruwanmu jiya talata a birnin na Kuala Lumpur.

Taron kolin na kasashen 'yan babu-ruwanmu ya bayyana adawar far ma kasar Iraqi da karfin soja ba tare da iznin Kwamitin Sulhun MDD ba, yana mai kira ga Iraqi da tayi aiki da bukatun majalisar na lalata muggan makamanta.

XS
SM
MD
LG