A yau laraba wasu 'yan bindiga suka shiga gidan wani hamshakin dan siyasar Nijeriya mai adawa da gwamnati, Harry Marshall, suka bindige shi har lahira, ana saura makonni 6 kafin a gudanar da zaben shugaban kasa.
Harry Marshall shine babban jami'in yakin neman zabe na dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ANPP, Muhammadu Buhari.
'Yan sanda sun ce ba a san ko su wanene 'yan bindigar ba, kuma an fara gudanar da bincike.
Masu magana da yawun jam'iyyar adawa ta ANPP sun dora laifin kashe Mr. Marshall a kan jam'iyyar PDP mai mulkin kasar. Jam'iyyar ta PDP ta ce tana mai yin tur da wannan kisa.
Mr. marshall yana daya daga cikin wadanda tun farko suka kafa jam'iyyar PDP dake rike da gwamnatin tarayya. A bara ya fice daga cikin jam'iyyar ya koma ANPP a saboda gardamar siyasar da ta kaure tsakaninsa da gwamnan jiharsu ta Rivers, Peter Odili.
Jihar Rivers tana daga cikin masu samar da arzikin mai a kasar. Mr. marshall sananne ne, kuma mai farin jini da tagomashi a idanun al'ummar yankin Niger Delta.
Rahotanni sun ce kashe Mr. Marshall da aka yi shine na babban dan siyasa na farko a tashin hankalin dake wakana kafin zaben da za a yi a wata mai zuwa. Zaben shine kuma zai zamo na farko da za a yi karkashin jagorancin fararen hula a cikin shekaru fiye da 20 a kasar.
Mutane da dama sun rasa rayukansu cikin 'yan watannin nan a fada tsakanin magoya bayan jam'iyyu dabam-dabam na Nijeriya.