Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Da Wakilin Paparoma Suna Tattauna Iraqi - 2003-03-05


Shugaba Bush zai gana yau laraba da wani wakilin Paparoma John Paul a fadar White House domin tattauna Iraqi.

Cardinal Pio Laghi zai isa fadar dauke da sakon dake kira ga shugaba Bush kada ya yaki kasar Iraqi daga Paparoma.

Kakakin fadar White House, Ari Fleischer, ya shaidawa 'yan jarida cewa shugaban yana mutunta bambancin ra'ayi kan batun Iraqi, amma kuma shine zai yanke shawarar karshe kan wannan batun.

A lokacin ganawar da ya saba yi kowane mako da jama'a ranar laraba a fadar Vatican, Paparoma John Paul yayi kira ga al'ummar duniya, ciki har da shugabanni, da su dauki dukkan matakan da zasu iya domin hana abkuwar wani yakin a duniya.

A yayin da mabiya darikar Katolika suke bukukuwan "Ash Wednesday" a fadin duniya kuma, Paparoma yayi kiran da a yi azumi domin tunawa da al'ummar kasar Iraqi wadanda suke shan bakar wahala a saboda takunkumin da MDD ta sanyawa kasar.

Fadar White House ta shugaban Amurka ta ki yarda da matsayin da fadar Paparoman ta dauka cewar yaki da kasar Iraqi ba ya da wata hujja ta shari'a ko kuma ta halalci. Fadar White House din ta ce ra'ayin shugaba Bush ne cewa yaki da Iraqi halal ne, wanda ke bisa shari'a kuma na kare rayukan Amurkawa.

XS
SM
MD
LG