Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babu Ruwan Jamhuriyar Nijar Da Iraqi - In Ji Hukumar Nukiliya Ta Duniya - 2003-03-07


Shugaban Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya ya ce takardun da aka bayar dake neman nuna cewa Iraqi ta yi kokarin sayen sinadarin nukiliya daga Jamhuriyar Nijar, na jebu ne.

Mohammed el-Baradei ya shaidawa Kwamitin Sulhun MDD a yau Jumma'a cewa hukumarsu ta zauna sosai ta nazarci takardun da aka gabatar domin karfafa wannan zargi, amma sai suka gano cewar takardun jebu ne. Ya ce a saboda haka hukumarsu ta cimma shawarar cewa wannan zargi da ake yi wa Nijar karya ne.

Hukumar ta binciki zargin da jami'an Amurka da na Ingila suka yi cewar sau biyu a cikin shekarun 1980 Iraqi tayi kokarin sayen makamashin Uranium daga Nijar. Har ila yau, jami'an Amurka sun yi zargin cewa a shekarar 2000, Nijar ta kulla yarjejeniyar sayarwa da kasar Iraqi makamashin Uranium a asirce.

Tun fari, Jamhuriyar Nijar ta karyata wannan zargi.

Har ila yau, Mohammed el-Baradei ya shaidawa Kwamitin Sulhun MDD cewar a bayan da suka shafe watanni uku suna bincike, har yanzu hukumarsu ba ta ga wata shaidar cewa Iraqi ta farfado da shirinta na kera makaman nukiliya ba.

XS
SM
MD
LG