Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Zata Jefa Kuri'ar Kin Amincewa Da Kudurin Bai Wa Iraqi Wa'adi - 2003-03-10


Ministan harkokin wajen Rasha, Igor Ivanov, ya ce kasarsa zata jefa kuri'ar kin yarda da wani kudurin Kwamitin Sulhun MDD wanda zai iya share fagen kai farmakin soja a kan Iraqi.

Mr. Ivanov ya shaidawa 'yan jarida yau litinin a birnin Moscow cewa daftarin kudurin ya kunshi matakan da ba za a iya cika su ba. Ya ce idan aka gabatar da wannan kuduri domin jefa kuri'a a kai, Rasha zata kada kuri'ar kin yarda.

Rasha tana da kujerar dindindin a cikin Kwamitin Sulhun MDD, kuma idan har ta jefa kuri'ar kin yarda, to ba za a zartas da wannan kuduri ba ke nan.

A karkashin tsarin jefa kuri'a na MDD, idan har mafi yawan wakilai 15 na Kwamitin Sulhu suka ki yarda da kudurin, to za a dauki kuri'ar Rasha a zaman na rashin yarda ne kawai. Amma kuma idan har mafi yawan wakilan majalisar suka amince da kudurin, amma Rasha ta jefa kuri'ar kin yarda, za a dauki wannan kuri'a a zaman hawa kujerar-na-ki.

Fadar White House ta ce tana fata Rasha ko Faransa ba zasu hau kujerar-na-ki ba. Kakakin fadar, Ari Fleischer, ya ce hawa kujerar-na-ki zata zarce abinda ya kira bacin rai kawai.

Ya ce a yau litinin, shugaba Bush yana buga waya ma shugabannin kasashen duniya a wani yunkurin ganin sun goyi bayan wannan mataki na Amurka da Britaniya, wanda zai bai wa Iraqi wa'adin nan da ranar litinin mai zuwa domin ta tabbatarwa da duniya cewa ba ta da makaman kare-dangi, ko kuma a kai mata farmakin soja.

XS
SM
MD
LG