Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Lallashin Kasashen Afirka Kan Kudurin Kai Wa Iraqi Harin Soja - 2003-03-10


Ministan harkokin wajen Faransa yana Afirka, inda yake lallashin kasashe uku masu kujera a cikin Kwamitin Sulhun MDD da su jefa kuri'ar rashin yarda da kudurin da zai share fagen kai farmakin soja a kan Iraqi.

A yau litinin Dominique de Villepin ya gana da shugaba Eduardo Dos Santos na Angola, daga baya kuma ya tashi zuwa kasar Kamaru, inda ya gana da shugaba Paul Biya.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ce shugaban Kamaru bai ce komai ba a bayan ganawar da yayi da Mr. de Villepin.

Shi ma ministan harkokin wajen Angola, Joao Miranda bai bayyana matsayin kasarsa ba, a bayan ganawar da suka yi da Mr. de Villepin a birnin Luanda. Amma kuma ya ce gwamnatin Angola ta yi imani da cewa yaki dai za a gwabza a Iraqi.

Mr. de Villepin zai kammala wannan ziyara tasa a kasar Guinea, inda zai gana da shugaba Lansana Conte.

A nan birnin Washington kuma, sakataren harkokin waje Colin Powell ya ci abincin rana tare da ministan harkokin wajen Guinea, Francois Fall. Guinea ce take rike da shugabancin Kwamitin Sulhun MDD a wannan watan.

Guinea da Angola da kuma Kamaru suna da matukar muhimmanci wajen ganin ko Amurka zata samu kuri'u 9 da take bukata domin zartas da wannan kudurin.

XS
SM
MD
LG