Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka, Britaniya Da Spain Zasu Yi Taron Koli Kan Batun Iraqi - 2003-03-14


Shugaba Bush da firayim ministocin Britaniya da Spain zasu yi taron koli a karshen makon nan domin tattauna dabarun yadda zasu bullowa kuri'ar da watakila zasu nemi MDD ta jefa kan Iraqi.

Fadar White House ta ce Mr. Bush zai gana da Tony Blair na Britaniya, da Jose Maria Aznar na Spain a tarayyar tsibiran Azores.

Amurka da Britaniya da kuma Spain sun gabatar da wani kuduri gaban Majalisar Dinkin Duniya, MDD, wanda zai bai wa Iraqi wa'adin nan da ranar litinin da ta tabbatarwa da duniya cewa ba ta da haramtattun makamai, ko kuma a kai mata farmakin soja.

Wazirin Jamus, Gerhard Schroeder, ya fada a yau Jumma'a cewar yayi imani za a iya warware rikicin na Iraqi ta hanyar lumana. Ya jaddada cewa sufetocin makamai na MDD zasu iya "kwance wa Iraqi damarar yaki ta hanya mai dorewa, wadda kuma za a iya tabbatarwa."

A cikin jawabin da yayi gaban majalisar dokoki a birnin Berlin, Waziri Schroeder ya ce a wannan lokaci, fiye da kowane lokaci a can baya, Jamus da Faransa da Rasha da kuma China, sun tabbatar da cewa za a iya raba Iraqi da makamanta, kuma tilas ne a yi hakan, cikin lumana.

Wadannan al'amura suna faruwa ne kafin a koma ga sabon zagayen tattaunawa a hedkwatar MDD a New York, inda jami'an diflomasiyya suke shirin tattaunawa kan wani daftarin kudurin da zai iay share fagen daukar matakan soja a kan Iraqi.

A jiya alhamis, wakilai 15 na Kwamitin Sulhun majalisar sun kasa cimma daidaiton ra'ayi kan wata sabuwar shawarar da Britaniya ta gabatar a bayan da aka shafe sa'o'i da dama ana tattaunawa.

A yau Jumma'a a birnin moscow, mukaddashin ministan harkokin wajen Rasha, Yuri Fedotov, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Interfax cewa shawarar ta Britaniya ba ta warware babbar matsalar da ake fuskanta ba, wadda a cewarsa ita ce ta samo hanyar hana yin amfani da karfin soja a kan Iraqi.

Faransa ta ce zata jefa kuri'ar hawa kujerar-na-ki kan duk wani kudurin da yake dauke da barazanar wa'adin kai farmakin soja. Sakataren harkokin wajen Amurka, Colin Powell, kuma, ya fadawa 'yan majalisar dokoki a jiya alhamis cewa watakila ma ba zasu nemi da a jefa kuri'a kan kudurin ba, idan har ya tabbata cewa Faransa zata hau kujerar-na-ki.

XS
SM
MD
LG