Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe 'Yan Kishin Falasdinu 5 A Yammacin Kogin Jordan - 2003-03-14


Sojojin bani Isra'ila sun kashe Falasdinawa 'yan bindiga su akalla biyar lokacin da suka kai farmaki kan wani gida a sansanin 'yan gudun hijira na Jenin dake yankin Yammacin kogin Jordan.

Majiyoyin Isra'ila da na Falasdinawa sun ce an kashe Falasdinawan su biyar a lokacin da aka goce da musanyar wuta yau Jumma'a da sanyin safiya, yayin da sojojin ke kokarin kama mutanen dake cikin wannan gida.

Falasdinawa suka ce hudu daga cikin wadanda aka kashe 'ya'yan kungiyar kishin Falasdinu ta "Islamic Jihad" ne, dayan kuma dan kungiyar 'yan shuhada'u ta al-Aqsa ne.

Jami'an Isra'ila suka ce sojoji sun gano makamai da rigunan sojojin Isra'ila a cikin gidan.

Sa'o'i kafin wannan, sojojin Isra'ila sun harbe 'ya'yan kungiyar Hamas su biyar a wani kauyen dake kusa da Jenin.

XS
SM
MD
LG