Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Madugun Juyin Mulkin Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya Ya Bayyana Kansa Shugaban Kasa - 2003-03-17


Wani tsohon hafsan sojojin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ya bayyana kansa a zaman shugaban kasar, bayan wani juyin mulkin da aka yi a lokacin da zababben shugaban yake kasar waje.

A lokacin da yake jawabi jiya lahadi a gidan rediyon kasar, Janar Francois Bozize, ya ce ya rushe gwamnati ya kuma dakatar da yin aiki da tsarin mulki. Yayi alkawarin gudanar da sabon zabe a bayan wa'adin mulkin rikon kwarya.

Tun fari a jiya lahadin, 'yan tawayen dake yaki ma Janar Bozize sun bayar da sanarwar kafa dokar hana yawon dare na tsawon kwanaki goma a Bangui, babban birnin kasar.

A ranar asabar, mayakan Janar Bozize suka kwace filin jirgin sama da fadar shugaban kasa a Bangui. Shugaba Ange-Felix Patasse yana ziyara a kasar Nijar a lokacin. A ranar asabar din, an yi harbi kan jirgin saman shugaban a lokacin da yake komawa birnin Bangui, abinda ya sa ala tilas ya sauka a kasar Kamaru, makwabciyarsu.

A yanzu haka, shugaba Patasse yana zaune a wani hotel dake Yaounde, babban birnin Kamaru. Ma'aikatan jakadanci sun ce yana shirin tafiya wani wurin. Mr. Patasse ya sha fuskantar yunkurin juyin mulki tun lokacin da aka zabe shi a 1993. A bara, sojojin Libya da 'yan tawayen Kwango sun taimaka masa wajen murkushe wani juyin mulkin da aka shirya tare da taimakon Janar Bozize.

Sojojin Libya sun bar kasar a watan Disamba, inda daruruwan sojojin kasashen Kungiyar Tarayyar tattalin Arzikin Yankin Tsakiyar Afirka, CEMAC, suka maye gurbinsu. An bayar da rahoton sojojin kiyaye zaman lafiya da dama a lokacin fadan na ranar asabar.

Kungiyar CEMAC da Tarayyar Kasashen AFirka sun yi tur da wannan juyin mulki.

An kori Janar Bozize daga kan mukamin babban hafsan sojojin kasar a watan Oktobar 2001, shi kuma ya zargi shugaba Patasse da rashin iya gudanar da mulki.

Shugaba Patasse ya zargi kasar Chadi da laifin goyon bayan yunkure-yunkuren juyin mulki na kwanakin baya a saboda rikicin da suke yi kan wani yanki mai arzikin man fetur a kusa da bakin iyakarsu.

XS
SM
MD
LG