Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sufetocin Makamai Na Majalisar Dinkin Duniya Sun Bar Iraqi - 2003-03-18


Sufetocin makamai na MDD sun isa kasar Cyprus yau talata bayan da aka kwaso su daga Iraqi bisa fargabar cewa yaki dai kam za a gwabza. Ana kwashe sauran ma'aikatan MDD dake can ma, a bayan da shugaba Bush na Amurka ya bai wa shugaba Saddam Hussein da 'ya'yansa wa'adin nan da gobe laraba da su bar Iraqi ko kuma a kai musu hari.

Wakilin Muryar Amurka a al-Qahira, Greg Lamotte, ya aiko da rahoton cewa wasu daga cikin sufetocin sun bayyana takaicin janye su da aka yi ba tare da sun kammala aikinsu ba. Wakilin namu ya ce cikin 'yan sa'o'i a bayan da babban sakataren majalisar, Kofi Annan, ya bada umurni, sufetocin makamai sun tattara nasu ya nasu suka shiga cikin kwambar motoci zuwa babban filin jirgin saman Saddam yau talata da safe.

Ma'aikatan MDD su 146, wadanda suka hada da sufetoci 56 da mataimakansu 80 sun isa filin jirgin inda wasu ke bayyana bakin ciki da takaicin cewa ba su kammala aikinsu na tabbatar da cewa an raba Iraqi da makamanta na kare dangi ba.

Kakakin sufetocin, Hiro Ueki, ya ce sufetocin sun yi bakin kokarinsu. Ya ce su a ganinsu, 'yan Iraqi sun ba su hadin kai sosai, kuma sun ga alamun karin hadin kai cikin 'yan kwanakin nan.

Amma kuma, Mr. Ueki ya ce tun da shugabanninsu ne suka yanke shawara, babu yadda suka iya, tilas su tattara su bar kasar.

A yau talata da safe suka bar Bagadaza suka tafi tsibirin Cyprus cikin wani jirgin MDD. Ana sa ran cewa wannan jirgi tare da wani na daukar kayayyaki, zasu kwashe sauran ma’aikatan MDD da suka rage a cikin Iraqi.

XS
SM
MD
LG