Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Iraqi Sun Yi Watsi Da Wa'adin Da Amurka Ta Bai Wa Saddam Hussein Cewa Ya bar Kasar - 2003-03-18


Shugabannin Iraqi sun yi fatali da wa'adin da shugaba Bush ya bai wa Saddam Hussein da 'ya'yansa maza biyu na su bar Iraqi ko kuma su fuskanci yaki.

Gidan telebijin na Iraqi ya ce an yi watsi da wannan wa'adin ne yau talata a lokacin wani taron hadin guiwa da aka yi na jam'iyyar Baath mai mulkin Iraqi, da kuma babbar majalisar zartaswar kasar da ake kira Majalisar Juyin Juya Hali.

Tun da fari, babban dan shugaba Saddam Hussein, Uday, yayi watsi da wannan wa'adin.

Kakakin fadar shugaban Amurka ta White House, Ari Fleischer, ya bayyana kin yarda da wa'adin a zaman kuskure na baya-bayan nan, kuma na karshe, na shugaba Saddam Hussein. Ya shaidawa 'yan jarida cewa har yanzu shugaba Bush yana fatar shugaban na Iraqi zai dauki wannan wa'adi na Amurka da gaske, ya kuma yi gudun hijira.

Kakakin bai musanta cewa tana yiwuwa Amurka ta kai farmaki kan Iraqi tun ma kafin cikar wa'adin kwanaki biyun da ta bai wa Saddam na gudun hijira ba. Wa'adin zai cika da karfe 2 na daren laraba (asubahin alhamis) agogon Nijeriya.

A wani gefen, sakataren harkokin wajen Amurka, Colin Powell, ya ce kasashe 45 sun shiga cikin ayarin kasashe masu goyon bayan kokarin Amurka na cire Saddam Hussein daga kan mulki. Mr. powell ya ce 30 daga cikin kasashen sun yarda a bayyana sunayensu, amma sauran sun ce kada a fadi sunayensu.

XS
SM
MD
LG