Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faransa da Rasha Sun Yi Tur Da Wa'adin da Shugaba Bush Ya Bai Wa Saddam Hussein - 2003-03-18


Faransa da Rasha sun soki wa'adin da Amurka ta bai wa shugaba saddam Hussein na Iraqi, amma kuma suna ci gaba da kokarin tuntubar Amurka.

Shugaba Jacques Chirac na Faransa ya ce babu wata hujjar yaki da kasar Iraqi, kuma yin haka barazana ce ga zaman lafiyar duniya da makomar yankin Gabas ta Tsakiya.

A cikin wani dan gajeren jawabi, shugaba Chirac ya ce wannan wa'adi na shugaba Bush barazana ce ga dangantakar kasa da kasa, yana mai cewa Iraqi dai ba ta yin wata barazanar da zata sanya a kai mata harin soja a wannan lokaci.

Shugaban na Faransa ya ce yin watsi da Kwamitin Sulhun MDD, tare da rungumar yin amfani da karfi maimakon dokoki na kasa da kasa sun dora alhaki mai yawan gaske a kan kasashen da zasu tsoma hannu wajen kaiwa Iraqi hari.

Wannan Allah wadarai na Mr. Chirac yayi kama da irin tur din da su ma shugabannin Jamus da Girka suka yi yau talata da matsayin na Amurka. Waziri Gerhard Schroeder na Jamus ya ce babu wani dalili na kawo karshen ayyukan binciken makamai a Iraqi.

Matsayin shugaban Faransa na yin adawa da matakan soja, yana samun goyon baya sosai a tsakanin al'ummar kasar, har ma masu fashin baki sun fara kamanta shi da gwarzon shugaban Faransa lokacin yakin duniya na biyu, Charles de Gaulle.

Kuri'un neman ra'ayoyin jama'a sun nuna cewa farin jinin shugaba Chirac a kasar ya cira sama zuwa kashi 74 daga cikin 100, farin jinin da babu wani shugaban kasar da ya taba yi im ban da de Gaulle.

Amma jakadan Faransa a Amurka, JJean-David Levitte, ya shaidawa gidan telebijin na CNN cewa idan Saddam Hussein yayi amfani da makamai masu guba a kan sojojin Amurka, to lamarin yana iya canjawa.

Fadar shugaban Rasha ta Kremlin ta ce shugaba Vladimir Putin yayi magana ta wayar tarho da shugaba Bush a yau talata, inda ya bayyana masa bacin ransa da wannan wa'adi da aka bai wa Saddam Hussein.

Amma shugabannin biyu sun yarda zasu ci gaba da tuntubar juna a kan harkokin duniya.

XS
SM
MD
LG