Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Zanga-Zanga A Nijeriya Sun Kona Gidan Wani Basaraken Gargajiya - 2003-03-18


'Yan zanga-zanga a yankin kudu maso yammacin Nijeriya sun kona gidan wani basaraken gargajiya a Jihar Ogun.

Wannan farmaki na jiya litinin a garin Shagamu, ya biyo bayan kashe wani shugaban matasa ne da 'yan banga suka yi.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ce an yi imani da cewa su wadannan 'yan banga, magoya bayan basaraken ne, Oba Michael Adeniyi Sonariwo.

Wani rahoton ya ce sarkin ya gudu kafin wadannan 'yan zanga-zanga su isa fadarsa.

XS
SM
MD
LG