Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Gwamnati Da Na 'Yan Tawayen Liberiya Suna Kece Raini - 2003-03-18


Sojojin gwamnati da na 'yan tawayen Liberiya suna gwabza kazamin fada na neman mallakar garin Gbarnga mai muhimmanci a gabashin kasar.

Wasu rahotanni sunce 'yan tawaye sun kwace gadar Saint Paul mai muhimmanci a kusa da garin na Gbarnga.

Ofishin kula da ayyukan jinkai na MDD ya ce wannan fada ya sa mutane dubu 15 sun gudu daga yankin. Ofishin ya ce a yanzu haka akwai mutane dubu 75 da suka rasa matsuguni a yankin arewa maso gabashin Liberiya. Da yawa daga cikinsu, sun doshi garin Kakata, wanda ke arewa da Monrovia, babban birnin kasar.

A bara, 'yan tawayen LURD na Liberiya sun kwace garin na Gbarnga, amma sai sojojin gwamnati suka sake kwatowa. A da, wannan gari shine hedkwatar madugun 'yan tawaye, Charles Taylor, wanda a yanzu shine shugaban kasar.

Tun shekarar 2000 'yan tawayen suke kokarin hambarar da gwamnatin Mr. Taylor.

XS
SM
MD
LG