Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Madugun Juyin Mulkin Jamhuriyar Tsakiyar Afirka Ya Ce Babban Muradinsa A Yanzu Shine Wanzar Da Tsaro - 2003-03-18


Madugun 'yan juyin mulkin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ya ce zai maido da mulkin dimokuradiyya da zarar an tabbatar da tsaro a kasar.

Janar Francois Bozize ya ce nan bada jimawa ba zai gana da jam'iyyun siyasa domin shirya zabubbuka, amma da farko sai an kawo karshen kwasar ganimar da ake yi. Har ila yau tsohon hafsan sojojin kasar ya nemi da a tura karin sojojin kiyaye zaman lafiya na Afirka da da sojojin Faransa zuwa kasar domin kwantar da fitina.

Janar Bozize ya bayyana wannan yau talata a Bangui, babban birnin kasar, a bayan da ya gana da ministocin harkokin wajen Gabon da Jamhuriyar Kwango.

Tashin hankali da kuma kwasar ganimar da ake yi tun bayan wannan juyin mulki na ranar asabar sun yi sanadiyyar mutuwar mutane 13.

Hambararren shugaba Ange-Felix Patasse ya nemi mafaka a Kamaru makwabciyarsu. Har yanzu bai ce komai ba, tun lokacin da aka hana shi komawa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a daidai lokacin da ake yi masa juyin mulkin.

A jiya litinin, tarayyar Kasashen Afirka ta ce tana nazarin dakatar da jamhuriyar Afirka ta Tsakiya har sai an maido da yin aiki da tsarin mulki a kasar. Ita ma Faransa, wadda ta yi wa kasar mulkin mallaka, ta yi tur da wannan juyin mulki.

XS
SM
MD
LG