Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ChevronTexaco Ya Dakatar Da Tonon Mai A Nijeriya - 2003-03-21


Kamfanin man fetur na Amurka mai suna ChevronTexaco ya dakatar da ayyukan tonon mai na reshensa a Nijeriya, bayan da aka shafe mako guda ana gwabza fadan kabilanci a yankin yammacin makwararar ruwan kogin Kwara, watau Niger Delta.

A cikin wata sanarwar da ya bayar da maraicen jiya alhamis, kamfanin man ya bayyana dakatar da ayyukan nasa a zaman matakin rigakafi domin tabbatar da lafiyar ma'aikatansa a tsakiyar wannan rikici da ake gwabzawa.

Kamfanin ya ce wannan rikici zai hana shi kai sauran man da aka yi oda na watan nan na Maris da watan Afrilu.

Wannan rikicin dai ya sa shi ma makeken kamfanin man Ingila da Holland mai suna Shell ya rage yaqwan man da yake hakowa. Kamfanonin suka ce yawan man da su biyu ke hakowa ya ragu da ganga fiye da dubu 266 a kowace rana a sanadin rikicin.

Kamfanonin na mai da kuma hukumomin Nijeriya sun kwashe daruruwan fararen hula da ma'aikata daga yankin na Niger Delta mai arzikin mai a bayan da aka yi mako guda ana fada. An kashe mutane akalla 11, ciki har da mata da yara.

Fitina ta barke a makon da ya shige a lokacin da wasu mayakan ruwan Nijeriya dake gadin cibiyoyin man fetur a yankin suka gwabza da wasu 'yan ta-kifen kabilar Ijaw. Su kuma wadannan 'yan ta-kife sai suka kai hari kan 'yan kabilar Itsekiri.

'Yan kabilar ta Ijaw sun bukaci kamfanonin mai da su biya su diyya. Suka ce kamfanonin mai suna gurbata musu wuraren kamun kifi.

XS
SM
MD
LG