Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tuhumi Wasu 'Yan Cuba Da Laifin Fashin Jirgin Sama Zuwa Florida - 2003-03-21


Hukumomin Amurka sun tuhumi wasu 'yan kasar Cuba shida da laifin yin amfani da wukake wajen yin fashin wani jirgin saman fasinjar Cuba zuwa tsibirin Key West na Jihar Florida a nan Amurka.

A jiya alhamis mutanen da ake tuhuma da fashin jirgin a ranar laraba suka bayyana a karon farko a gaban kotu. Kowanne daga cikinsu yana fuskantar hukumcin da ba zai kasa shekaru 20 ba a kurkuku idan an same shi da laifi.

Jami'an Amurka suka ce mutanen shida sun yi fashin wannan jirgin sama karami mai farfela biyu a lokacin da ya tashi daga tsibirin Isle of Youth zuwa Havana, babban birnin kasar ta Cuba.

Akwai fasinja kimanin dozin uku a cikin wannan jirgi, wanda ya sauka kalau a tsibirin Key west karkashin rakiyar wasu jiragen saman yakin Amurka.

Cuba ta bukaci da a gaggauta mayar mata da wannan jirgi nata tare da dukkan mutanen dake cikinsa. Har yanzu ba a san dalilan mutanen na yin fashin wannan jirgi ba.

XS
SM
MD
LG