Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iraqi Ta Ce Saddam Hussein Da Iyalansa Suna Nan Kalau - 2003-03-21


Ministan yada labaran Iraqi, ya ce shugaba Saddam Hussein da iyalansa ba su samu koda kwarzane ba a lokacin da sojojin Amurka suka kai farmaki kan gidansa.

Mohammaed Saeed al-Sahaf ya shaidawa 'yan jarida yau Jumma'a a birnin Bagadaza cewa an kai harin ne kan wani gida na shugaba Saddam Hussein, amma babu abinda ya same shi ko iyalansa.

Jami'an Amurka sun ce sun yi imani shugaban na Iraqi yana cikin wani gida tare da dukkan 'ya'yansa ko kuma wasu daga cikinsu, a lokacin da sojojin kawance suka cilla makamai masu linzami da bama-bamai kan wannan gida, a hare-haren farko na asubahin alhamis.

XS
SM
MD
LG