Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijeriya ta Tura Sojojinta Domin Kwantar Da Fitina A Yankin Niger Delta - 2003-03-21


Majiyoyin soja da shugabannin al'umma a yankin kudu maso gabashin Nijeriya, sun ce mutane akalla 60 aka kashe a ranar alhamis kawai, a kazamin fadan kabilancin da ake yi a can.

Majiyoyin sun bayyana wannan adadi a yau Jumma'a, kwana guda a bayan da hukumomi suka tura jiragen sama domin kwashe fararen hular dake tserewa daga fadan da ake gwabzawa a tsakanin kabilun Ijaw da Itsekiri a yankin Niger Delta mai arzikin man fetur.

Amma kuma ba a san zahirin yawan mutanen da suka mutu ba tun lokacin da fada ya barke mako gudan da ya shige. Gwamnatin Nijeriya ta tura sojoji kimanin dubu daya zuwa yankin.

Kamfanin man fetur na ChevronTexaco na Amurka ya dakatar da ayyukan tonon mai a rijiyoyinsa dake Nijeriya a sanadin wannan rikici.

Har ila yau, wannan fada ya sanya shi ma kamfanin man Shell ya rufe tasoshin famfon mai da yawa, ya kwashe ma'aikatansa, sannan ya rage yawan man da yake hakowa a kowace rana. Haka kuma, kamfanonin biyu sun kwashe daruruwan mazauna kauyukan yankin ta jiragen sama.

Wannan tashin hankali ya barke a makon da ya shige, a lokacin da sojojin ruwan Nijeriya masu yin sintiri suna gadin cibiyoyin mai suka fatattaki wasu 'yan ta-kifen kabilar Ijaw. Daga nan 'yan ta-kifen suka kai farmaki kan 'yan kabilar Itsekiri.

A ranar laraba, shugaba Olusegun Obasanjo yayi gargadin cewa yawan tashe-tashen hankulan siyasa a kasar yana barazana sosai ga zaben shugaban kasar da za a gudanar a cikin wata mai zuwa.

Mutane fiye da dubu 10 sun mutu a tashe-tashen hankulan siyasa da na kabilanci da aka yi tun lokacin da gwamnatin Mr. Obasanjo ta hau kan karagar mulki a 1999, bayan mulkin shekaru 15 na soja.

XS
SM
MD
LG