Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Rufe Karamin Ofishin Jakadancinta Dake Lagos, Nijeriya, Ga Jama'a - 2003-03-21


Amurka ta kara matakan tsaro a babban ofishin jakadancinta da kuma karamin ofishin jakadancin dake Nijeriya.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce ta rufe karamin ofishin jakadancinta dake cibiyar kasuwanci ta kasar, Lagos, ga jama'a, ma'ana ba zata gudanar da wani aiki ba. Haka kuma, ta rage yawan ma'aikatan dake ofishin jakadancinta a Abuja, babban birnin kasar.

An yanke wannan shawara ce a saboda fargabar tsaro a yayin da Amurka take kai farmakin soja kan Iraqi.

Fiye da rabin mutane kimanin miliyan 129 na Nijeriya Musulmi ne.

XS
SM
MD
LG