Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Taron Dangi Sun Ci Gaba Da kai Hare-Hare Kan Bagadaza Da Biranen Arewacin Iraqi - 2003-03-24


Sojojin taron dangi sun yi luguden wuta daga sama a kan birnin Bagadaza a yau, yayin da fada ya kara rincabewa a arewacin kasar.

An yi ta jin kararrakin fashe-fashe tun da sanyin safiya, har zuwa tsakar rana yau litinin a Bagadaza. Fadar shugaba Saddam Hussein tana daya daga cikin wuraren da aka kai wa farmaki a yau din.

A cikin dare kuma, zaratan sojojin Amurka sun dira a yankin arewacin Iraqi, yayin da jiragen yakin kasashen taron dangi suka kai hare-hare kusa da birnin Kirkuk.

A kudancin kasar kuma, jami'an Amurka sun ce an kashe sojoji akalla 9, aka kama ko aka kashe wasu 12 lokacin da aka yi kwanton-bauna aka far musu kusa da Nasiriyya.

Jami'an Amurka sun kuma ce wani jirgin helkwafta na yaki samfurin "Apache" ya bace, amma ba su ce komai ba game da makomar mayakan dake ciki.

A cikin wani jawabin da yayi ga al'ummar Iraqi ta telebijin, shugaba Saddam Hussein ya ce maharan sun raina kurwar al'ummar Iraqi, kuma zasu dandana kudarsu.

Daga bisani, gidan telebijin na Iraqi ya nuna wani jirgin saman yakin Amurka na helkwafta samfurin "Apache" a wani fili kusa da birnin Bagadaza. Ba a san abinda ya sami mayakan dake cikin jirgin ba.

Sojojin taron dangi suna kuma gwabzawa da sojojin Iraqi a wurare da dama a kudancin kasar. Syria ta ce wani makami mai linzamin da Amurka ta harba ya fada kan wata motar safa ta fasinja a cikin Iraqi, ya kashe Syriyawa 5 fararen hula, ya raunata wasu guda goma.

XS
SM
MD
LG