Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Man Chevron-Texaco Na Amurka Ya Rufe Kusan Dukkan Ayyukansa A Nijeriya - 2003-03-24


Makeken kamfanin man fetur na Amurka mai suna Chevron-Texaco ya rufe kusan dukkan ayyukansa a Nijeriya, yayin da 'yan ta-kifen wata kabila suka yi kashedin kara zub da jini a arangamar da suke yi da jami'an tsaro.

Kamfanin Chevron-Texaco ya bi sahun kamfanonin mai na Royal Dutch/Shell da Total-Fina-ELF wadanda tun farko suka rufe akasarin cibiyoyin mansu a Nijeriya.

Wannan shine karon farko a cikin kwanaki 10 da aka yi da barkewar wannan fitina, da aka samu labarin rufe rijiyoyin mai dake cikin teku, wadanda tun farko aka dauka ba su fuskantar hadari daga tashe-tashen hankulan da ake yi a yankin.

Da ma, yawan man da Nijeriya take hakowa a kowace rana ya ragu da kashi 16 daga cikin 100 kafin wannan shawara ta Chevron-Texaco.

Matasa 'yan ta-kifen kabilar Ijaw a yankin Niger Delta sun yi barazanar ragargaza cibiyoyin mai idan har jami'an tsaro suka ci gaba da kai farmaki a kauyukansu. Wani kakakin rundunar sojan Nijeriya ya ce an kama mayakan kabilar Ijaw fiye da 12 wadanda suka yi wannan barazana.

Tashin hankalin da ya barke a makon da ya shige tsakanin 'yan kabilar Ijaw da kabilar Itsekiri da kuma jami'an tsaro, ya haddasa mutuwar mutane dama, ciki har da sojoji biyun da aka kashe ranar asabar.

XS
SM
MD
LG