Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Larabawa Sun Bukaci Da A Kawo Karshen Farmakin Da Ake Kaiwa Iraqi - 2003-03-25


Ministocin harkokin wajen kasashen larabawa sun yi kira ga Amurka da Britaniya da su gaggauta janye sojojinsu daga Iraqi.

Ministocin na kungiyar kasashen larabawa sun yi wannan kiran a lokacin da suka gana a birnin al-Qahira, domin tattauna wannan farmaki da sojojin taron dangi ke kaiwa a cikin Iraqi.

Wakilan na kungiyar kasashen larabawa sun amince da wani kuduri wanda ya ce harin da aka kai kan Iraqi ya sabawa dokokin Majalisar Dinkin duniya, MDD, ya kuma sabawa muradun kasashen duniya.

Babban sakataren kungiyar, Amr Moussa, ya ce kungiyarsu zata dauki wanann batu zuwa gaban MDD, yana mai cewa, "Mu kasashen larabawa, zamu bukaci Kwamitin sulhun MDD da ya gana domin ya dauki shawarar kawo karshen wannan yaki, tare da bada umurnin janye sojojin kasashen waje."

XS
SM
MD
LG