Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Musulmi Suna Bayyana Adawa Da Yaki A Iraqi - 2003-03-28


Fusatar da Musulmi ke nunawa a Masallatai game da yakin da Amurka take jagoranci kan Iraqi, ta bazu zuwa kan titunan kasashen Musulmi a yau Jumma'a.

A bayan hudubobin yin Allah wadarai da limamai suka gabatar a cikin Masallatai lokacin sallar Jumma'a, Musulmi sun fito kan tituna domin bayyana adawarsu da wannan yakin da suke dauka a zaman hari kan dan'uwa Musulmi.

A Iran, kasar da ta gwabza mummunan yaki na tsawon shekara takwas da makwabciyarta Iraqi, dubban Iraniyawa sun bazu kan titunan birnin Teheran a yau Jumma'a domin zanga-zangar da gwamnati ta amince da yinta ta nuna adawa da yaki.

A birnin al-Qahira, mutane fiye da dubu 15 sun yi maci ta cikin tsoffin unguwannin birnin daga Masallacin al-Azhar, bayan da aka idar da sallar Jumma'a.

A zirin Gaza da yankin Yammacin kogin Jordan, dubban Falasdinawa sun kona mutum-mutumin shugaba Bush na Amurka, da na firayim minista Tony Blair na Britaniya da kuma na firayim ministan Bani Isra'ila Ariel Sharon.

A can nahiyar Asiya kuwa, 'yan zanga-zanga sun cika tituna suna daga murya domin bayyana adawarsu da wannan yaki.

A cikin biranen kasashe kamar Indiya, Pakistan da Bangladesh, dubban 'yan zanga-zanga sun yi maci cikin lumana. A Indonesiya, kasar da ta fi kowacce yawan Musulmi a duniya, 'yan zanga-zanga sun nuna fusatarsu ta hanyar yin kira ga jama'a da su kauracewa kayayyakin Amurka.

XS
SM
MD
LG