Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Jakadan Saudi Arabiya A Ivory Coast - 2003-03-28


Hukumomin Ivory Coast sun fara gudanar da binciken kisan jakadan Sa'udiyya a wannan kasa dake Afirka ta Yamma.

'Yan sanda sun ce a yau Jumma'a da sanyin safiya direban jakada Mohammed Ahmed al-Rasheed ya tsinci gawar maigidan nasa tsirara cikin jini.

Da alamun an kashe jakadan ne a cikin wannan gini mai tsaro sosai a Abidjan, babban birnin kasar. Wannan gini yana dab da ofishin jakadancin Amurka a kasar.

Jami'ai suka ce sun yi imani an kashe jakadan ne a cikin dare, lokacin da ake aiki da dokar hana yawon daren da aka kafa a sanadin tawayen da aka yi watanni shida da farawa a kasar.

XS
SM
MD
LG