Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Nijeriya Yayi Barazanar Tsare Masu Tayar Da Fitina A Niger Delta - 2003-03-28


Shugaba Olusegun Obasanjo na Nijeriya ya ce ya umurci dakarun tsaro da su kama mutanen dake da hannu a rikice-rikicen kabilancin da suka gurgunta masana'antar man fetur mai matukar muhimmanci ga kasar.

A cikin furucinsa na farko tun lokacin da wannan fada ya barke, Cif Obasanjo ya fada a yau Jumma'a cewa yana kokarin maido da kwanciyar hankali a yankin na Niger Delta.

Nijeriya ta girka sojojinta suna yin sintiri a wannan yankin.

A baya cikin watan nan 'yan ta-kifen kabilar Ijaw a yankin suka fara gwabzawa da jami'an tsaro, daga baya kuma suka far ma 'yan kabilar Itsekiri, wadanda suka zarga da laifin goyon bayan gwamnati.

Mutane akalla 60 sun mutu a wannan gumurzun.

'Yan kabilar ta Ijaw sun ce zasu kawo karshen wannan fada, a bayan da suka tattauna da jami'an gwamnatin Jihar Delta a farkon makon nan.

Wannan rikici ya sa ala tilas kamfanonin mai sun dakatar da ayyukansu a kasar, matakin da ya katse yawan man da Nijeriya take hakowa kowace rana da kashi 40 daga cikin 100.

XS
SM
MD
LG