Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tarzomar siyasa a  Nigeria - 2003-03-31


Ana fargabar cewa wasu mutane sun halaka a Nigeriya bayan fadan da aka caba tsakanin magoya-bayan jam'iyyun dake adawa da juna a yankin Niger Delta na Nigeriya dake fama da tashin-tashina.

Shedun gani da ido sun ce fadan ya barke ce a lokacin da magoya-bayan jam'iyyar PDP mai mulki suka yi dirar-mikiya akan wani taron siyasa da magoya-bayan jam'iyyar adawa ta ANPP suke yi a garin Bakana dake kusa da garin Fatakwal mai arzikin Mai.

Tulin mutane sun fada cikin wani Kogi domin tserewa wannan fada, kuma ana fargabar duk sun nutse sun halaka. Wannan tarzoma ta ranar asabar itace ta baya-baya a jerin irinta da suka zama ruwan Dare a gabannin babban zaben majalisar dokokin kasar da za a yi a ranar 12 ga wannan Wata na Afirilu.

XS
SM
MD
LG