Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Kundumbalar Amurka Sun Kwato Fursunar Yaki - 2003-04-02


Zaratan sojojin Amurka sun kwato wata mace sojar Amurka wadda ake rike da ita a zaman fursunan yaki a Iraqi.

Janar Vincent Brooks na hedkwatar sarrafa ayyukan yaki na Amurka shi ya bayyana wannan a wani taron 'yan jarida na ba-sabam ba a cikin dare a hedkwatarsu dake Qatar.

An bayyana cewa wannan soja, farabiti ce mai suna Jessica Lynch, wadda kafin kwato ta aka bayyana ta a zaman wadda ta bace a bakin daga.

Daga baya, Janar Brooks ya nuna hoton bidiyo na kwato sojar da aka yi, yana mai cewa sojojin kundumbalar sun kuma gano gawarwaki 11 a wannan hari da suka kai na kwato sojar a wani asibiti na Iraqi.

Ya ce ba a san ko akwai Amurkawa cikin gawarwakin ba, kuma kwararrun masana kimiyya zasu nazarci gawarwakin.

manyan mukarraban gwamnatin shugaba Bush sun bayyana kwato farabiti Lynch da aka yi a zaman babban labari, suna mai bayyana cewawannan kasa tana alfahari da sojojin da suka kwato ta.

XS
SM
MD
LG