Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Wani Dan Kasuwar Nijeriya A Tashin Hankalin Da Ake Jin Yana Da Alaka Da Siyasa - 2003-04-02


Hukumomin Nijeriya sun bada sanarwar dake cewa an kashe wani dan kasuwa a tashin hankali na baya-bayan nan da ake jin cewa yana da alaka da manyan zabubbukan da za a gudanar cikin wannan wata.

Jami'ai suka ce ranar asabar da daddare, wasu 'yan bindiga sun kashe Yemi Oni a gidansa a garin Ado Ekiti a Jihar Ekiti dake kudu maso yammacin Nijeriya. Mr. Oni jigo ne cikin magoya bayan gwamnan jihar ta Ekiti, Adeniyi Adebayo, wanda yake neman da a sake zabensa bisa wannan kujera. Mutanen biyu sun halarci wani taron siyasa tare ranar da aka kashe shi. 'Yan sanda suna binciken wannan kisa.

A watan da ya shige, wasu 'yan bindiga sun kashe wani jigon jam'iyyar hamayya ta ANPP, Harry marshall, a gidansa.

Nijeriya ta shirya fara gudanar da zabubbuka na farko da fara hula zasu shirya cikin shekaru 20 a ranar 12 ga watan nan na Afrilu, inda za a fara da zaben 'yan majalisun dokoki. mako guda bayan wannan, za a gudanar da zaben shugaban kasa da na gwamnoni.

A halin da ake ciki, uwar kungiyoyin Kwadago ta Nijeriya, NLC, ta janye yajin aikin da ma'aikatan gwamnati suka shirya gudanarwa, wanda kuma yayi barazanar kara rage yawan man da kasar ke hakowa.

An shirya fara yajin aikin jiya talata, amma sai shugabannin kwadago suka cimma yarjejeniya da gwamnati domin kawo karshen sabani kan yawan albashin da za a ringa biyan ma'aikatan.

XS
SM
MD
LG