Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Birnin Bagadaza Ya Fada Hannun Sojojin Amurka - 2003-04-10


Tankokin Yakin Amurka da motocin Yakinsu masu sulke suna ci gaba da kafa sansanoni a cikin Birnin Bagadaza a yau Alhamis, kwana guda bayan faduwar gwamnatin Saddam Hussien a lokacin da sojojin Amurka suka kutsa kai cikin birnin.

Jiya Laraba, wasu tarukan mutane cikin murna sun sheke da rawa akan titunan birnin, inda suka ringa kayar da Mutum-Mutumin Saddam Hussien na Tagulla.

To amma bayan da suka gama murnarsu, akasarin "yan kasar ta Iraqi sun koma cikinm gidajensu inda suka kulle kawunansu, saboda tsoro ko fargabar kwasar gamina da karyewar doka da Odar da zasu biyo baya. Shugaba Bush ya ce sojojin taron dangin sun samu nasarar tarihi a Bagadaza, to amma ya yi kashedin cewa har yanzu ba a kawo karshen yakin na Iraqi ba. Shi ma fraiministan Birtaniyya Tony Blair ya ce ya yi murna da jin cewa an ci birnin na Bagadaza. Ministan harkokin wajen kasar Kuwait ya yabawa sojojin taron dangin a karkashin Amurka saboda gagarumin sadaukar da Kan da suka yi da 'yantar da kasar Iraqi.

XS
SM
MD
LG