Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gobe Za a Fara Zabe a Nigeriya - 2003-04-10


A gobe(Asabar) ne za a yi zabe a Nigeriya, bayan da wata kotun tarayya ta yi watsi da wasu kararrakin da aka shigar ana kabulantar halascin gudanar da zaben.

Wannan ne karo na farko da gwamnatin farar hula zata gudanar da irin wannan zabe a cikin shekaru 20, to amma kuma ana fama da matsalolin kayan aiki da tangarda wajen tsarawa da gudanar da zaben.

Fiye da mutane miliyan 60, ne zasu zabi wakilan majalisun dokokin kasar a zagaye farko na Zaben a gobe Asabar.

Akwai jam'iyyun siyasa guda 30 dake fafutukar haye kujerun majalisar wakilai data Dattijai na kasar. A ranar 19 ga wannan Wata na Afirilu ne za a gudanar da zaben shugaban kasar.

Daga cikin matsalolin kayan aikin da ake fama da su a wannan Zabe a wannan kasa wacce ta fi kowace yawan jama'a a nahiyar Afirka har da jinkirin da ake samu a ko ina a kasar wajen raba Katin Zabe da kuma fargabar da kasar ta shiga a sakamakon fadace-fadacen kabilanci da addini a yankunan kasar a ciki har da yankin Niger Delta mai arzikin Mai.

A shekarar 1999 ne gwamnatin sojin kasar ta gudanar da irin wannan babban zabe wanda shugaba Olusegun Obasanjo, dan Kudancin kasar ya lashe. Yanzu, akwai 'yan takara guda 19 da suka shiga zaben shugabancin kasar. To amma wanda ya fi kowane dan takara tagomashi, shine Muhammdu Buhari, tsohon shugaban mulkin sojin kasar, dan arewa. Masu lura da al'amurra sun ce watakila shine zai lashe zaben.

A farkon watan jiya na Maris aka kashe wani babban mai goyon bayan Alhaji Mohammdu Buhari. A cikin wannan Mako ne rundunar 'yan Sandan kasar ta gabatar da wasu mutane da ta ce 'yan fashi da makami ne da ta ce sune suka kashe Chief Harry Marshall.

XS
SM
MD
LG